Babban sakatare na MDD Ban Ki-moon, ya sanar a ranar Laraba da kafa kwamitin kasa da kasa da aka dorawa nauyin gudanar da bincike kan ayyukan keta hakkin dan adam a kasar Afrika ta Tsakiya CAR tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2014.
Kwamitin binciken ya kunshi manyan kwararru uku da suka hada da mista Acho Castaneda, 'dan kasar Mexico, madam Fatimata M'Baye, 'yar kasar Mauritania da kuma Bernard Acho Muna, 'dan kasar Kamaru wanda kuma shi ne zai jagoranci wannan kwamitin, in ji kakakin Ban Ki-moon.
Kwamitin tsaro na MDD, a cikin wani kudurin da ya cimma a ranar 5 ga watan Disamban shekarar 2013, ya bukaci mista Ban da ya kafa cikin gaggawa wani kwamitin bincike na kasa da kasa bisa wa'adin da aka tsai da na farko na tsawon shekara daya domin yin bincike bisa rahotonnin da aka samu dake bayyana ayyukan keta hakkin dan adam da na jin kai a kasar Afrika ta Tsakiya, da taimakawa wajen gano masu hannu kan wadannan ayyukan aika aika da kuma gurfanar da su gaban kotu.
Mambobin uku na wannan kwamitin za su isa birnin New-York nan ba da jimawa ba, inda za su gana mista Ban Ki-moon, daga baya, su isa birnin Geneva, sannan su wuce birnin Bangui. (Maman Ada)