in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zabi Catherine Samba-Panza a matsayin sabuwar shugabar mulkin wucin gadi a CAR
2014-01-21 10:04:26 cri

Madam Catherine Samba-Panza, dake rike da magajin garin Bangui, ta lashe zabe a ranar Litinin a matsayin sabuwar shugabar mulkin wucin gadi a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR tare da samun kuri'u 75 bisa masu zabe 129 a yayin zaben sirri na kwamitin rikon kwarya na kasa (CNT) dake matsayin wata majalisar wucin gadi da aka kafa tun cikin shekarar 2013 a yayin wani zaman taro na musammun na kusan mako daya a cibiyar majalisar dokokin kasar dake birnin Bangui.

Madam Samba-Panza, mai shekaru 54 da haifuwa, ta kasance mace ta farko da aka zabe ta a wannan babban matsayi tun lokacin da kasar Afrika ta Tsakiya ta samu 'yancin kanta a shekarar 1960.

An zabe ta zagaye na biyu a gaban abokin takararta mista Bilal Desire Nzanga-Kolingba, dan tsohon shugaban kasar Andre Kolingba mai shekaru 57 da haifuwa, bayan ta samu kuri'u 64 a zagayen farko gaban abokin takararta wanda ya samu kuri'u 52. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China