Sojojin kasar Chadi na tawagar kasa da kasa dake Afrika ta Tsakiya CAR wato MISCA sun fara ficewa daga Bangui a ranar Talata domin isa arewacin kasar, tun bayan da aka bude wuta kan masu zanga-zangar kin jininsu a birnin Bangui, inda aka kashe fararen hula 'yan kasar Afrika ta Tsakiya da jikkata wasu da dama, da kuma musanyar wutar da sojojin Chadin suka yi tare da sojojin kasar Burundi a ranar Litinin, a cewar wata majiyar tsaro.
Rukunin sojojin dake kushe da mutane 850, ya kasance na farko dake cikin tawagar sojojin kasa da kasa na tsakiyar Afrika (FOMAC) da kungiyar kasashen tattalin arzikin shiyyar tsakiyar Afrika ta tura shekarun baya domin taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya, ana zargin sojojin Chadi da hada kai tare da tsoffin 'yan tawayen Seleka dake mulkin kasar yanzu wajen aikata kisa da kwashe dukiyoyin jama'a.
A cewar hedkwatar sojojin MISCA dake karkashin janar Martin Tumenta Chomu, 'dan kasar Kamaru da manyan jami'an tsaron Afrika ta Tsakiya, tura su zuwa arewacin Afrika ta Tsakiya na daga cikin ayyukan tagawar na tabbatar da tsaro da hada kan wannan kasa dake tsakiyar Afrika da ta fada cikin tashin hankali tun bayan kama ikon Michel Djotodia a ranar 24 ga watan Maris a Bangui. (Maman Ada)