A cewarsa hakan ya biyo biyan bukatar da ake da ita, ta gyara kura-kuran da suka shafi shirye-shiryen gudanar zaben.
Djinnit yace jam'iyya mai mulkin kasar ta Guinea, da jam'iyyar adawa sun cimma ra'ayi guda kan jinkirta ranar zaben, kuma kwamitin kula da harkokin zaben kasar mai zaman kansa, wanda aka dorawa alhakin shirya zaben majalisar dokokin ya riga ya fara ayyukan gyare-garen da suka wajaba.
Daga nan sai jami'in MDD ya yi kira ga shuwagabannin jam'iyyun kasar ta Guinea, dama al'ummar kasar, su bada cikakken goyon bayansu ga gudanar zaben dake tafe, ta yadda zai kammala lami lafiya kuma cikin nasara.
Tun dai yayin babban zaben shugabancin kasar na shekarar 2010 ne, ake ta samun bambancin ra'ayoyi tsakanin jam'iyyar dake mulki da jam'iyyar adawa a kasa ta Guinea, musamman kan harkokin da suka shafi gudanar da zaben majalisar dokokin kasa, matakin da ya tilasta jinkirta zaben har sau biyar. Muddin dai aka samu nasarar gudanar da zaben a wannan karo, hakan zai kawo karshen yanayin rikon kwarya da hukumar kasar ke ciki. (Maryam)