Manazarta siyasar kasar dai na cewa nasarar zaben a wannan karo zai kawo karshen gwamnatin rikon kwarya da ake ciki a kasar, bayan nasarar zaben shugaban kasa da aka gudnar a shekarar 2010 da ta gabata.
An dai ta dage zaben 'yan majalissun kasar ne tun a shekarar 2010, duk kuwa da cewa bisa doka ya dace a gudanar da shi tsakanin watanni 6 da zaben shugaban kasa. Dage zaben dai na da nasaba da sabanin da jam'iyyun siyasar kasar suka rika samu don gane da yanayin gudanarsa.
A baya bayan nan ma an dage zaben da aka shirya gudanarwa ran 24 ga wata, domin samar da karin lokacin shiri, ya kuma saba da ranar tunawa da kisan gilla da dakaru masu biyayya ga rundunar shugaban juyin mulkin sojin kasar Moussa Dadis Camara suka yi wa dimbin fararen hula, tare da yi wa wasu mata da dama fade.
Yanzu haka dai 'yan takarar kujerun wakilcin majalissar dokokin 114 ne suka shiga wannan zabe, ciki hadda 'yan takarar jam'iyyar RPG ta shugaba Alpha Conde, da jam'iyyar UFDG wadda Cello Dalein Diallo ke jagoranta, da kuma jam'iyyar UFR dake karkashin jagorancin Sidya Toure. (Saminu Hassan)