A wannan rana kuma, mataimakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Rasha Igor Morgulov ya bayyana yayin da yake ganawa da jakadan kasar Koriya ta arewa dake kasar Rasha cewa, kasar Rasha ta yi kira ga kasar Koriya ta arewa da ta kwantar da hankali, kuma kada ta dauki matakan tsananta halin da ake ciki a yankin Koriya. Kafin wannan, shugaban kasar Rasha Vładimir Putin ya taba bayyana cewa, bai kamata bangarori daban daban da abin ya shafa su dinga tsananta halin yankin Koriya ba, ya kamata su warware matsaloli ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka John Forbes Kerry ya bayyana yayin da yake ziyara a kasar Koriya ta kudu a ranar 12 ga wata cewa, kasar Amurka tana son yin shawarwari tare da kasar Koriya ta arewa ta hanyar yin shawarwari a tsakanin bangarori shida ko kuma shawarwari a tsakanin bangarorin biyu, amma ya kamata kasar Koriya ta arewa ta bi ka'idojin kasa da kasa. (Zainab)