Wani rahoto da babban bankin duniya ya fitar na nuna cewa, tattalin arzikin nahiyar Afirka na ci gaba da habaka, duk kuwa da tarin matsalolin fatara, da rashin daidaito dake wanzuwa tsakankanin al'ummomin nahiyar.
Rahoton ya bayyana hasashen da wani bankin samar da ci gaba dake birnin Washington ya yi na cewa, yankin kudu da hamadar Sahara na iya samun karuwar tattalin arziki da kaso 4.9 bisa dari a bana, sakamakon karuwar harkokin cinikayyar daga sassa masu zaman kansu, wanda jimillar kudin da ya kunsa ke kaiwa dalar Amurka miliyan dubu 33 a ko wace shekara.
Har ila yau rahoton ya sanya karin harkokin zuba jari daga tsagin gwamnatocin yankin, da bunkasar sassan hakar ma'adanai da noma, da sauran sassan ayyukan hidima a matsayin fannonin dake dada yiwa tattalin arzikin yankin kaimi.
Bugu da kari rahoton na babban bankin duniya da aka fitar gabannin taron shekara-shekara da bankin ke gudanarwa da hadin gwiwar bankin ba da lamuni na IMF, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar Juma'a mai zuwa, ya ce, ma'aunin tattalin arziki na GDP a yankin na kudu da hamadar Saharar zai karu da kaso 5.3 a badi, yayin da kuma ake sa ran sake karuwarsa da kaso 5.5 a shekarar 2015.
Sai dai duk da wannan hasashe na ci gaba da ake wa yankin, a hannu guda rahoton ya nuna halin matsi da kangin talauci da al'ummarsa ke ciki, inda ya bayyana yiwuwar karuwar hakan da kaso 16 zuwa 30 bisa dari a shekarar 2030 dake tafe. (Saminu)