140116murtala
|
A Yau Alhamis ne, shugaba Goodluck Ebele Jonathan na tarayyar Najeriya ya sauke wasu manyan hafsoshin sojojin kasar nan, sa'annan ya maye gurbinsu da wasu sababbi.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaba Goodluck Jonathan wato Reuben Abati ya fitar.
Shugaba Jonathan ya nada Air Marshal Alex Badeh a matsayin sabon babban hafsan dakarun tsaron kasar, inda ya maye gurbin Admiral Ola Sa'ad Ibrahim.
Har wa yau kuma, Manjo-Janar Kenneth Minimah shi ne sabon hafsan dakarun kasa inda ya maye gurbin Laftanar Janar Azubike Ihejirika.
An kuma nada Rear Admiral Usman O. Jibrin a matsayin sabon babban hafsan sojojin ruwan Najeriya, wanda ya maye gurbin Vice Admiral Dele Joseph Ezeoba. Bugu da kari, Air Vice Marshal Adesola Nunayon Amosu ya maye gurbin Air Marshal Badeh a matsayin babban hafsan dakarun saman kasar ta Najeriya.
Ana ganin cewa dai an sauke shugabannin sojojin ne saboda gazawarsu wajen magance matsalar tsaron da ke ciwa jama'a tuwo a kwarya a Najeriya.
Sanarwar da Mista Reuben Abati ya fitar ta ce, dukkan sauye-sauyen da aka yi sun fara aiki ne nan take. (Murtala Zhang)