140115murtala
|
Shugaban kungiyar tsoffin sojoji 'yan mazan jiya na jihar Yobe Kaftin Zakari Garba mai ritaya ya yi yabo saboda yadda gwamnatin jihar ta Yobe ke kula da harkokin kungiyar wajen samarwa mambobinta abubuwan tallafawa rayuwarsu daidai gwargwadon hali.
Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa da Kaftin Ibrahim Ladi Gadine mai ritaya ya wakilta a wajen bikin tunawa da ranar 'yan mazan jiyan da aka yi a babban dakin taro na WAWA dake gidan gwamnatin jihar a garin Damaturu.
A cikin jawabin sa Kaftin Zakari Garba mai ritaya ya bayyana cewa sanin kowa ne cewa a duk shekara ana irin wannan biki na tunawa da 'yan mazan jiya ne ba don komai ba sai don jinjina ma irin rawar da suka taka wajen tsare rayuka da dukiyoyin al'umma da kuma hobbasansu na kokarin kare diyaicin kasar nan don ci gaba da kasancewar ta a matsayin kasa daya al'umma daya.
Ya ce wannan kungiya tasu a kullum suna alfahari da irin ayyukan ciyar da al'umma gaba da gwamnatin Alhaji Ibrahim Geidam ke yi, wajen gudanar da ayyukan raya kasar da suka hada da gina hanyoyin mota a birni da karkara, da samar da ruwan sha, da inganta harkokin ilmi da na kiwon lafiya da makamantansu.
Sai dai kuma ya tunasar da gwamnan jihar kan koke-koken da suka gabatar a shekarar bara na neman a sama musu da matsugunin da za su rika haduwa wato ofishi don tafiyar da ayyukan kungiyarsu, da kuma motar sufuri don rage musu wasu wahalhalun da suka fuskanta wajen huldar yau da kullam na kungiyar.
A martanin sa dangane da bukatun kungiyar ta 'yan mazan jiya da kuma bayaninsa dangane da wannan rana ta tunawa da 'yan mazan jiya, gwamnan jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam wanda kwamishinan harkokin cikin gida da yada labaran jihar Alhaji Goni Fika ya wakilta, ya ce wannan rana ta tunawa da 'yan mazan jiya rana ce mai muhimmanci.
A cewar Gwamnar, ba don komai ba sai don ganin irin muhimmiyar rawar da 'yan mazan jiyan suka taka dangane da zaman lafiyar duniya a yakin duniya na farko da na biyu, da kuma yadda suka jajirce wajen ganin sun kare diyaicin kasar nan daga yakin basasar da aka yi fama da shi a baya, da kuma yadda a yanzu suke kokarin samar da zaman lafiya a kasa.(Murtala)