in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kungiyoyin kwallon kafar Najeriya sun jimanta mutuwar tsohon shugaban kungiyar Kano Pillars
2014-01-12 16:08:12 cri

Kungiyar shugabannin kungiyoyin kwallon kafar kasar Najeriya sun bayyana jimaminsu sakamakon mutuwar tsohon shugaban kungiyar Kano Pillars, Alhaji Sani Usman, wanda ya mutu a asibitin kasa dake Garki, Abuja.

Cikin wani jawabin da sakataren kungiyar na riko, Alloy Chukwuemeka ya fitar a Ilorin, ya bayyana cewa mutuwar ta jijjiga kungiyar, inda ya bayyana mamacin a matsayin dan kungiyar dake ba da gudummawa a kowane lokaci.

Chukwuemeka ya mika ta'aziyya a madadin kungiyar ga iyalan mamacin, shugabannin kungiyar Kano Pillars, gwamnati da al'ummar Kano baki daya. Sa'annan ya yi addu'ar Allah madaukakin sarki ya gafarta masa, ya kuma ba wa iyalansa hakurin jure rashin.

Sa'annan kungiyar ta wakilta 'ya'yanta uku, don zuwa Kano yin ta'aziyyar ga iyalan tsohon shugaban na Pillars. Jami'an uku sun hada da Sabo Babayaro, shugaban kungiyar Kaduna United, Abba Yola, shugaban kungiyar Kano Pillars da Zanna Mala, shugaban kungiyar Elkanemi Warriors ta Maiduguri.

Marigayi Sani Usman kafin mutuwarsa, ya taba zama manajan daraktan gidan rediyon jihar Kano, da kuma manajan janar na rediyo Gotel, jihar Adamawa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China