A lokacin ganawarsu, Mista Zhao ya ce cikin shekaru 43 bayan da kasashen 2 suka kulla huldar diplomasiyya, bangarorin 2 suka samu damar raya huldar dake tsakaninsu sosai, da hadin kai a fannoni daban daban tare da samar da sakamako mai kyau. Kasar Sin ta dora muhimmanci ga kokarin raya huldar dake tsakanin kasashen 2.
A nasa bangaren, shugaba Obiang ya ce, ana gamsuwa da ci gaban huldar dake tsakanin kasashen 2, kana Equatorial Guinea na nuna ma kasar Sin godiya kan tallafin da ta dade tana baiwa kasar Equatorial Guinea.(Bello Wang)