"Wannan baje koli yana cikin tsare tsaren bukukuwan kasa na cikon shekaru 52 da kasar Benin ta samu 'yancin kai, kuma wata dama ce ta yin musanya taskanin manoma da jama'a, nuna daraja da kuma nuna yabo ga kayayyakin da ake kerawa a kasar Benin, da kuma sanar da wata hanyar bunkasuwa wajen fitar da wadannan kayayyaki zuwa kasashen waje", in ji madam Madina Sephou.
Haka kuma a yayin wannan baje koli za a gudanar da ayyuka daban daban musamman ma tarurukan kara ma juna sani, ranakun kungiyar UEMOA, Togo, ECOWAS da kuma Ghana. (Maman Ada)