Rashin samun abinci mai gina jiki zai janyo wa kasar Benin a cikin shekaru goma asarar tattalin arziki mai tarin yawa, wanda aka kiyasta zuwa kimanin kudin Sefa biliyan 913 in ji shugaban kwamitin kasa mai kula da harkokin abinci, mista Jean Kokou Tossa a ranar Asabar a birnin Cotonou.
' A tsawon shekaru goma, idan ba'a yi komi ba, asarar da za'a samu a fuskar tattalin arzikin a kasar Benin dake da nasaba da rashin abinci mai gina jiki ga mutanen kasar za ta cimma kudin Sefa biliyan 52 sakamakon rashin sanadarin Iode, Sefa biliyan 131 sakamakon jinkirin girma, kana Sefa biliyan 730 sakamakon rashin sanadarin Fer wato kusan kimanin Sefa biliyan 913 baki daya' in ji mista Jean Kokou Tossa. (Maman Ada)