in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi gagarumin bikin murnar shigowar sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin a birnin Ikkon Najeriya
2014-01-12 16:06:55 cri


Ranar Asabar 11 ga wata ne, aka yi gagarumin bikin murnar shigowar sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin a birnin Lagos na tarayyar Najeriya.

Akwai jami'an kasashen Sin da Najeriya da dama wadanda suka halarci wannan kasaitaccen buki, ciki har da jakadan kasar Sin dake Najeriya Mista Deng Boqing, sabon karamin jakadan kasar Sin dake Lagos Mista Liu Kan, da shugaban hukumar kula da masu shige da fice ta tarayyar Najeriya Mista David Parradang, gami da wakilai na kamfanonin kasar Sin daban-daban a Najeriya.

Har wa yau kuma, akwai shugabannin kungiyoyin Sinawa dake zaune a kasashen Ghana, Cote d'Ivoire, Mali da Guinea wadanda suka zo nan birnin Lagos na Najeriya don halartar bikin.

A yayin jawabin da ya gabatar, jakada Deng Boqing ya bayyana cewa, sakamakon kokarin da al'ummomin Sin da Najeriya suka yi, dangantakar abokantaka dake tsakaninsu na bunkasa cikin sauri a halin yanzu. Tare da karatowar sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin ta 2014, Mista Deng ya nuna gaisuwa da fatan alherinsa ga mahalarta bikin, kuma yana fatan jama'ar Sin da Najeriya za su kara kuzari wajen habaka hadin-gwiwa da mu'amala tsakaninsu a nan gaba.

A wajen bikin, an gayyaci wata babbar tawagar masu fasaha daga lardin Heilongjiang na kasar Sin don su nuna wasanni masu kayatarwa, ciki har da raye-raye da kade-kade na gargajiya, da wasan lankwasa jiki wato acrobatics a Turance, da sauransu. Masu nuna fasaha daga Najeriya su ma sun gabatar da raye-rayen gargajiya, ciki har da wata rawar gargajiya ta Hausa-Fulani, wadda ta jawo hankalin masu kallo sosai.

A wajen taron kuma, na samu damar zantawa da shugaban hukumar kula da masu shige da fice ta tarayyar Najeriya Mista David Parradang, don jin ta bakinsa game da gagarumin bikin da aka yi. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China