Hasashen da wani masanin tattalin arziki dan kasar Amurka yayi game da wasu jerin kasashe hudu da tattalin arzikinsu zai habaka ya ja hankalin wasu 'yan Najeriya
|
Dama dai Mr. John shine yayi hasashen cewa kasar Sin da Indiya da Brazil da Africa ta kudu tattalin arzikin su zai bunkasa a duniya, wanda a yanzu haka wannan hasashe nasa ya zama gaskiya.
To a yanzu ma wannan masani ya sake makamancin wancan hasashe inda ya lasafta wasu kasashe masu tasowa su hudu dacewa nan gaba kadan suma tattalin arzikin su zai buwaya, kasashen kuwa sun e Mexico, Indonisiya ,Nigeria da Turkiya wanda a dunkule ake masu lakabi da MINT.
Ya kare wannan hasashe nasa da wasu hujjoji guda uku wato yawan albarkatun kasa da yawan jama`a da kuma fadin kasa wanda duk wadannan kasashe hudu suna da shi.
Mr John Olin ya cigaba dacewa wadannan kasashe hudu sune zasu karbe ragamar tattalin arzikin duniya nan da `yan wasu shekaru kadan masu zuwa, to amma a tattaunawar da yayi da manema labarai wani malami a sashen nazarin harkokin tattalin arziki na jami`ar Bayero da ke Kano farfesa Abubakar Garba Sheka ya bayyana shakkun Najeriya zata iya kasancewa cikin jerin wayan can kasashe sabo da wasu dalilai nasa daya zayyana.
Dalilan sun hada da rashin iya jagoranci daga wajen shugabanni da cin hanci da karba rashawa da kuma rashin yin amfani da albarkatun kasa da ake da su yadda ya kamata.
To sai dai Farfessa Abubakar Garba Sheka ya kawo hanyoyin da Najeriya ya kamata ta bi domin ganin ba a barta a baya ba na cimma hasashen da Mr Olin masanin tattalin arziki dan kasar Amurka ya yi.
Farfesa Abubakar Garba Ibrahim Sheka ke nan na sashen nazarin harkokin tattalin arziki a jami `ar Bayero dake Kano a arewacin Najeriya.(Garba Abdullahi Bagwai)