Wani jami'in tsaron gwamnatin kasar ya bayyana cewa, a wannan rana da dare, 'yan ta'adda sun kai wa mista Droui hari kusa da kasuwar dake cibiyar birnin Sirte, inda suka lugudan wuta kan motar dake ciki tare da kashe shi.
Birnin Sirte shi ne yankin marigayi shugaban kasar Moammar Gadhafi, tun bayan yakin basasa tare da kifar da gwamnatinsa, har yanzu ana samun dakarun dake adawa da sabbin hukumomin kasar ta Libiya, lamarin dake kawo zaman zullumi a wannan yanki tun bayan rikicin kasar. Mista Droui shi ne mataimakin ministan masana'antun kasa, kuma ya taba zama mamban kwamitin wucin gadi na kasar Libya dake yankin Sirte. (Maryam)