Bisa labarin da kamfanin dillanci labarai na kasar Sin Xinhua ya aiko mana, an ce, 'yan tawaye suna ci gaba da janye jiki daga babban birnin kasar Libya wato Tripoli a ranar Alhamis din nan bisa ga aniyar da majalissar dokokin kasar ta dauka na ganin ta fitar da duk 'yan tawaye daga babban birnin kasar.
Kungiyar 'yan tawayen mai suna Special Deterrence Force ta mika hedkwatarta dake gabashin Tripoli ga babban hafsan rundunar sojin kasar Libya a ranar Alhamis din nan, in ji wata majiyar tsaro.
Firaministan kasar Ali Zeidan ya halarci bikin mika wannan ofishi a filin saukar jiragen sama na sojoji a Mitiga, yana mai cewa, mika ofishin hade da kayayyakin dake ciki da 'yan tawayen suka yi, wani cigaba ne da aka samu a kokarin hada kasar gu daya.
An kafa kungiyar 'yan tawayen Special Deterrence Force ne a shekara ta 2011 lokacin da 'yan tawaye da tsohuwar gwamnati ke tashin hankali na gama gari, yanzu dai kungiyar a hukunce ta zama ofishin yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi da hana faruwar laifukan da suka jibanci hakan.
Bisa bin umurnin majalissar dokokin kasar, 'yan tawayen sun fara janye jiki daga Tripoli, gwamnati kuma ta riga ta kafa dokar ta baci a birnin na Tripoli don ba da kariya ga 'yan tawaye masu dauke da makamai su samu ficewa lami lafiya har nan da ranar Asabar. (Fatimah)