in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 10 sun halaka a rumbun adana makamai a Libya
2013-11-29 15:45:26 cri

Gwamnan gundumar Brak Wadi Shati da ke kudancin kasar Libya Birgediya Mohamed Al Dahabyi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, wata fashewar da ta faru a wurin ajiye makamai ranar Alhamis da yamma, wadda ta haddasa mutuwar mutane 10, kana wasu 15 suka jikkata.

Jami'in ya ce, a ranar Asabar da ta gabata ma, sai da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka yi kokarin kutsawa wurin ajiye makaman, inda suka yi awon gaba da makamai.

Gundumar ta Brak Wadi Shati, tana da nisan kilomita 60 ne kudu da birnin Sabha, babban birnin lardin Fezzan.

Bayanai na cewa, mahukuntan yankin kudancin Libya suna kokarin kwace yankin da 'yan sumogan bakin haure ba bisa ka'ida ba da masu sayar da miyagun kwayoyi da kuma makamai suka mamaye.

Gwamnatin rikon kwaryan Libya, ta shata wani tsari game da tsaron kan iyaka, inda aka dorawa tawagar bayar da agaji kan harkokin kan iyaka ta kungiyar tarayyar Turai (EUBAM) da ke Libya, alhakin horas da dakarun kan iyaka na Libya, ko da ya ke har yanzu ba su isa yankin kudancin kasar ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China