Mahukuntan kasar Libya sun bayyana aniyarsu, ta kulla yarjejeniyar tsaron kan iyakoki da kasar Sudan.
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar ta Libya kanar Abdul Razzaq al-Shihabi ne, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru da ya gudana a birnin Tripoli. kanar Al-Shihabi ya kara da cewa, za a rika lura da kan iyakokin kasashen ne ta hanyar amfani da na'urorin dake aiki da tauraron dan adam mallakar kasar Italiya.
A ranar Larabar da ta gabata ma dai sai da ministan tsaron Najeriya ya ziyarci kasar ta Libya, inda ya tattauna batutuwan da suka shafi hadin gwiwar tsaron iyakokin kasashen biyu da takwaransa na kasar ta Libya. (Saminu)