Kasar Libya ta yi watsi da wani shiri na kwamitin tsaro na MDD na tura wani rukunin sojojin tsaro dake kunshe da mutane 235 domin kare tawagar MDD dake Tripoli, babban birnin kasar, in ji Tarek Mitri, wakilin musamman na MDD a kasar Libya, kana shugaban tawagar ba da tallafi ta MDD dake kasar Libya a ranar Talata (UNSMIL).
Da yake magana a yayin wani taron manema labarai a cibiyar MDD dake birnin Tripoli, mista Mitri ya bayyana cewa, ana mai da hankali kan adadin wannan rukunin sojoji da karfinsa, da ma aikin da zai yi, domin kwantar da fargaba domin kaucewa duk wata jita-jita da wasu kalaman da ba su da tushe, in ji sanarwar UNSMIL.
Mista Mitri ya kara cewa, shirin na kwamitin tsaro na MDD da aka ba da labarinsa a karshen watan Nuwamba, ya biyo bayan karin bacin ran jama'ar kasar Libya, bayan lamarin zubar da jini da ya abku a birnin Tripoli a lokacin zanga-zangar lumana domin korar kungiyoyin dakarun sa kai dake babban birnin.
Aikin wannan rukunin sojojin MDD, an takaita shi, kuma kafa wannan rukunin soja mataki ne da aka saba gani a sauran tawagogin diplomasiyya kuma yana zuwa daidai da sharudan yarjejeniya kan matsayin aikin tagawar MDD da aka sanya hannu tare da gwamnatin kasar Libya, in ji wannan jami'in na MDD dake kasar Libya. (Maman Ada)