A ranar 6 ga wata, a fadar shugaban kasar Nijeriya, jakadan kasar Sin dake kasar Deng Boqing wanda zai kammala aikinsa a kasar da uwargidansa sun yi ban kwana da shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan.
Jakada Deng ya mika gaisuwar sabuwar shekara ta shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Goodluck Jonathan, kuma ya nuna godiya ga taimakon da gwamnatin Nijeriya da jama'arta suka nuna wa aikinsa a cikin shekaru uku da suka gabata. Ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, an kara habakar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya, kuma an kara kafa amincewar juna a fannin siyasa, da yalwata hadin gwiwa a tsakaninsu, kuma zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu na samu karfafuwa. Yanzu, kasashen Sin da Nijeriya suna fuskanci babban aikin samun bunkasuwa, kuma akwai makoma mai haske wajen raya hadin gwiwa dake tsakaninsu. Ya yi imani cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu za ta samu makoma mai haske.
Shugaba Jonathan ya yi godiya ga sakon gaisuwa daga shugaban Xi, kuma ya bukaci jakadan Deng da ya isar da sakon gaisuwarsa ga shugaba Xi, kana ya waiwayi ziyarar aikin da ya yi a kasar Sin da kuma ziyarar da shugaban majalisar wakilan jama'a ta Sin Zhang Dejiang ya kai a kasar Nijeriya, ya bayyana cewa, Nijeriya ta dora muhimamnci sosai game da alakar da ke tsakaninta da kasar Sin, kuma, tana fatan yin kokari tare da kasar Sin, don aiwatar da daidaito da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, tare da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a cikin harkokin duniya da na shiyya-shiyya, da kuma hadin gwiwa ta moriyar juna daga dukkan fannoni, ta yadda za a yalwata dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen Nijeriya da Sin.(Bako)