A ranar Laraba 8 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta Nijeriya ta shirya liyafar ban kwana ma jakadan kasar Sin Deng Boqing a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, inda sakataren ma'aikatar Martin Ihoeghian Uhomoibhi, da mataimakinsa Godwin Agama suka halarta.
Har ila yau Darektan hukumar kula da baki ta ma'aikatar ,jakada Usman Baraya, Darektan hukumar kula da harkokin Asiya da tekun Pasifik, Adekunbi A.Sonaike-Ayodeji, da wasu jakadun kasashen waje dake Nijeriya sama da 30 duk sun halarci wannan liyafa.
A jawabin sa Mista Martin Ihoeghian Uhomoibhi ya bayyana cewa, Nijeriya da Sin sun dade suna sada zumunci tsakanin su kuma suna taimakawa juna na tsawon lokaci domin neman samun 'yanci da tabbatar da zaman lafiya.
A nasa bangare shima , jakada Deng Boqing mai barin gado a jawabinsa ya lura da cewa gwamnatocin kasashen biyu suna kokarin tabbatar da sakamakon da aka samu a ganawar shugabanninsu, da sa kaimi ga hadin gwiwa a fannoni daban daban, a kokarin bude wani sabon babi na sada zumunci tsakanin su. Ya yi imani cewa, bayan kokarin jama'arsu cikin dogon lokaci, za a cimma burin kasashen biyu yadda ya kamata.(Fatima)