in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin jihar Yobe dake Najeriya za ta bada magani kyauta ga masu fama da cutar dundumi
2014-01-06 16:21:17 cri

Gwamnatin jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya da hadin-gwiwar shirin samar da muradun karni na MDD (MDGs) sun dukufa kan samar da kiwon lafiya mai inganci ga al'umma nan da shekara ta 2020, ta hanyar bada magani kyauta da kuma yin aikin tiyata ga masu fama da cutar dundumi kimanin 2200 a jihar.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin darakta janar na hukumar kula da kiwon lafiya a mataki na farko (PHC) na jihar ta Yobe Alhaji Lawan Kawu Ibrahim wanda babban jami'in hukumar Sani Zagam ya wakilta a tattaunawarsu da manema labaran jihar a ofishinsa dake birnin Damaturu.

Daraktan hukumar ta PHC ya ce, tuni aka duba masu dauke da cutar ta dundumi kimanin 850 wadanda ya zuwa suka fara gani sosai sakamakon wannan aiki na ido da aka yi musu.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ce ta dauki nauyin yiwa mutane 2000 masu fama da cutar ta dundumi aiki a yayin da shirin muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya(MDGs) ya dauki nauyin mutane kimanin dari biyu wadanda bisa jimmila ya kai mutane 2200 da za'a tallafawa.

Alhaji Lawan Kawu ya ci gaba da cewar, tiyatar da za a yiwa masu dauke da cutar ta dundumi za'a gudanar da ita ne a manyan asibitocin dake a garururwan Damaturu,Potiskum , Gashua da kuma garin Gaidam.

Don haka, yayi kira ga al'ummomin dake fama da irin wannan cuta ta dundumin ido da su hanzarta zuwa wadannan asibitoci don samun magani da kuma aikin na ido kyauta.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China