Xi ya ce, kamata ya yi kasashen Sin da Habasha su karfafa mu'amala tsakanin manyan jami'ansu, da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a muhimman fannoni. Sin ta nuna goyon baya ga Habasha wajen shiga kungiyar cinikayya ta duniya WTO.
Ban da haka, Xi ya taya wa kungiyar AU murnar cika shekaru 50 da kafawa, ya ce, Sin za ta nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen samun ci gaba tare.
A nasa bangare, firaministan kasar Habasha Hailemariam ya ce, Sin ta kafa manufarta kan Afirka bisa adalci, girmamawa juna, da kuma moriyar juna. Dukkan kasashen nahiyar suna maraba sosai da wannan tsari. Da fatan za a karfafa dangantakar abokantaka a duk fannoni tsakaninsu bisa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, a kokarin samun ci gaba tare. Habasha za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen sa kaimi ga raya dangantaka tsakanin bangarorin biyu.
A wannan rana kuma, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Zhang Dejiang shi ma ya gana da mista Hailemariam a birnin Beijing.(Fatima)