Bikin lalata hauren giwan wanda shi ne karo na farko a kasar Sin,ya nuna kokarin da gwamnati take yi na hana cinikin hauren giwa bada izini ba,da kuma bukatar dake akwai na wayar da kan jama'a wajen kare namun daji.
Hauren giwayen da ba'a kai ga sarrafa su ba da kuma wadanda aka riga aka kankare aka yi ma ado wadanda gwamnati ta kwace a cikin shekarun da suka gabata an tara su gu daya ne tare da nike su.
Wannan aikin dai hukumar kula da gandun daji da sha'anin mulki na shige da fice na kasar ta gudanar. (Fatimah Jibril)