An bayar da wannan sanarwar ce yayin taron manema labarai da aka yi a birnin Istambul na kasar Turkiya, taron da ya samu halartar mambobin kawancen 'yan adawar Syria(SNC).babbar kungiyar 'yan adawar kasar Syria da ke gudun hijira a kasashen waje da kuma wakilan kungiyar malaman addinin musulunci ta kasa da kasa.
Bayanai na nuna cewa, dukkan manyan motocin dakon kayan, sun hallara a yankunan Hatay,Gaziantep da Santiurfa da ke kan iyakan kasar Turkiya tun ranar Talata, kuma za su shiga kasar Syria ranar Laraba saboda yanayi a kasar da yaki ya daidaita ba shi da kyau a halin yanzu.
Kimanin kungiyoyin fararen hula na gida da kasa da kasa 36 ne suka shiga cikin shirin samar da kayayyakin agajin wanda gidauniyar kare 'yancin bil-adama da samar da tallafin jin kai ta kasar Turkiya(IHH) ta kirkiro da nufin ceto rayuwar bil-adama,inda aka tara kayayyakin agajin da ya kai dala miliyan 1.
A cewar rahotannin MDD na baya-bayan nan,'yan gudun hijirar kasar ta Syria sun kai miliyan 6, inda 600,000 daga cikin suna zaune ne a kasar Turkiya, kuma ana saran adadin zai kara ninkawa ya zuwa karshen shekara ta 2014.(Ibrahim)