140105bagwai
|
Rashin kwanciyar hankali a jahohin Borno da Yobe da rikita-rikitar sisaya game da yajin aikin malaman jami'o'i na daya daga cikin abubuwan da suka faru a shekarar data gabata wadanda ba za'a taba mantawa da su ba, inji Farfesa Kamilu Sani Fagge na jami'ar Bayero dake arewacin Najeriya.
Farfesan ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon CRI.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce babu shakka zai yi wahala ga duk wani dan Najeriya ya manta da halin da kasar ta tsinci kanta a cikin na rashin tabbas a 2013.
Ya ce kwamacalar siyasa da hare- haren kungiyar boko haram da kuma matsalolin da sha'anin ilimiya fuskanta a manyan jami'o'in kasar sun kasance abin kaico a kasa kamar Najeriya da take a matsayin uwa ga sauran kasashen dake Nahiyar Afrika.
Farfessa Kamilu Sani Fagge yayi bayani a dunkule game da yadda ya nazarci yanayin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki a shekara ta 2013 inda jam'iyyun adawa suka dunkule wuri guda domin yakar jam'iyya mai jan ragamar mulkin kasar, tare da fatan samun sauyin mai ma'ana a cikin shekarar da muke ciki a halin yanzu.
Batun cin hanci da rashawa, batu ne da ya jima yana dakile ci gaban Najeriya, wanda shi ma yana daya daga cikin mahimman abubuwan da suka faru a 2013.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ci gaba dacewa babu shakka wannan magana ta Tsohon shugaba Obasanjo zata jima tana tasiri ga tsarin demokuradiyyar Najeriya musamman a daidai lokacin da ake ta yada bayanai game da sake tsayawar shugaba Jonathan a babban zaben kasar da za'a yi cikin shekarar badi.(Garba Abdullahi Bagwai)