Rahotanni daga Najeriya sun ce, sojojin kasar sun tabbatar da hallaka 'yan kungiyar Boko Haram akalla guda 63, bayan da 'yan kungiyar suka kai hari a barikin sojin na garin Bama a jihar Borno dake arewacin kasar, in ji babban darektan sashin yada labaran rundunar ranar jiya Litinin.
Sojojin, in ji Manjo Janar Chris Olukolade, sun kai hari ta kasa da ta sama a kan mobayar 'ya'yan kungiyar a wani daji dake Alafa mai nisan kilomita 21 daga Bama, abin da ya zama wata babbar nasara da aka samu a kan kungiyar.
Manjo Janar Olukolade ya ce, rundunar sojin kasar tana ta kai hari a kan dukkan inda ake zaton maboyar 'yan kungiyar ne a cikin watanni biyu da suka gabata, sannan kuma adadin 'ya'yan kungiyar ya kai 50 da sojoji suka kashe a cikin kwanaki 10 da suka gabata a lokacin arangama da aka yi a jihar ta Borno. (Fatimah)