Mukaddashin minista a ma'aikatar harkokin wajen tarayyar Najeriya Viola Onwuliri, ta yi kira ga daukacin ofisoshin jakadancin kasashen waje dake karbar kudin shirya Visa da kudaden waje, da su dakatar da hakan ba tare da wani bata lokaci ba.
Viola Onwuliri ta yi wannan kira ne yayin ganawarta da wasu wakilan ofisoshin diplomasiyyar kasashen ketare dake Najeriyar, jiya a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, gabanin fara bukukuwan cikar kasar shekaru 100 da kafuwa.
A cewar ministar, tuni suka samu labarin cewa, wasu daga ofisoshin diplomasiyyar na karbar harajin shirya Visa da kudaden ketare, wanda hakan ya sabawa dokar kasar, da ma ikon na kasancewa mai cikakken ikon cin gashin kai.
Wannan dai batu na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da ofishin jakadancin kasar Birtaniya dake Najeriyar, ya bayyana cewa, daga 16 ga watan Disambar nan, ofishin zai fara karbar kudaden shirya Visar kasarsa ne, da dalar Amurka a maimakon Naira da ake amfani da ita a Najeriyar. (Saminu)