Rundunar sojin Najeriya ta ce, wani bata-kashi da ya auku tsakanin dakarun sojin kasar da 'ya'yan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, ya haddasa rasuwar mutane sama da 70 a garin Bama dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
Dauki ba dadin da sassan biyu suka shafe sa'o'i da dama suna yi a safiyar Juma'ar da ta gabata dai, ya biyo bayan farmakin da maharan kungiyar Boko Haram suka kaiwa barikin sojin dake garin Bama. An ce, maharan sun fito ne daga garin Banki dake kusa da iyakar kasar da Kamaru, sun kuma yi amfani da nau'o'in makamai daban daban yayin da suka yiwa barikin sojin dirar mikiya, inda kuma nan take sojojin suka mai da martani da manyan makamai.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin daraktan rundunar sojin mai lura da harkokin yada labaru Manjo Janar Chris Olukolade, ta ce, dauki ba dadin na ranar Juma'a ya haddasa rasuwar sama da 'yan bindigar 50, da sojoji 15 da kuma fararen hula 5. (Saminu)