A Nigeriya, adadin mai da ake sata duk rana a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur ya ragu daga ganga 100,000 zuwa ganga 40,000 a duk rana, in ji gwamnan jihar Delta Emmanuel Uduaghan.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar kasar a ranar Alhamis din nan 2 ga wata jim kadan bayan ganawarsa da shugaban Nigeriya Goodluck Jonathan, gwamna Uduaghan ya ce, duk da cewa, wannan adadin ma yana da yawa kwarai da gasket, amma idan gwamnati ta kara tsaurara matakan tsaro, za'a kara samun raguwar fiye da hakan.
Ya yi bayanin cewa, idan an kama masu satar mai tare da masu hukunci mai tsanani yadda ya kamata, a sa'i daya, a samar da ingantattun na'urorin da za su lura da wuraren, to, za'a samu raguwar satar kwarai da gaske.
Satar mai a Nigeriya dai ya zama ruwan dare a yankin Niger Delta mai arzikin mai. (Fatimah)