Mashaya da aka kai hari yana da nisan kilomita kimanin 25 daga birnin Mombassa, inda mutane da yawa suke murnar sabuwar shekara, wassu mutane 3 ne dai kusa da hanyar mashaya suka jefa gurnati, nan take, suka kuma tsere da babur.
Wani jami'in 'yan sanda na wurin ya bayyana cewa, lamarin ya zama wani harin ta'addanci kuma sai dai ya zuwa yanzu, babu wata kungiya ko jama'a da ya dauki alhakin kai harin. Amma wassu na ganin cewa, harin da aka kai ya yi kama da harin da kungiyar Al-shabab ta yi a baya.
Tun daga shekarar 2011, bayan da gwamnatin Kenya ta tura sojoji zuwa Somaliya don murkushe kungiyar Al-shabab da ke da alaka da ayyukan ta'addanci, Kenya ta zama wani wurin da ke fama da harin ta'addanci sosai, yanzu an kai hare-haren ta'addanci da dama a mashaya, da wuraren ibada, da tasoshin motar fasinja. (Bako)