Rikicin na wannan karo da ya shafi kabilu uku ya kwashe kusan mako guda ana bata kashi tsakanin bangarorin uku. A cikin 'yan shekarun nan, wadannan kabilu guda 3 sun yi ta rikici tsakaninsu bisa dalilin albarkatun ruwa da gonaki.
Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta Kenya ta bayyana cewa, rikicin da ya haddasa mutanen da yawansu ya kai kimanin dubu 32 kaura daga gidajensu, kana kuma dubun dubantar mutane sun ketara zuwa kasar Habasha da ke makwabtaka da kasar ta Kenya domin neman mafaka.
Gwamnatin yankin Marsabit ta sanar da cewa, a cikin watanni 4 da suka gabata, rikicin kabilu ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 100.(Bako)