Dubban mazauna galibi mata, yara da tsofaffi sun kaurace ma gidajen su dake bakin iyaka sakamakon jita jitar da ake yadawa na daukar fansa.
Kwamandan rundunar 'yan sandan yankin Moyale, Nehemiah Lagat ya ce an riga an tura daruruwan jami'an 'yan sanda a wannan yanki domin shawo kan al'amarin.
Wannan kashe kashe dai ya zo ne kwanaki biyu bayan da wani ma'aikacin wannan yanki na Moyale aka mashi yankan rago, aka kuma kashe wani mai gadin gida a unguwar Karare da ke Marsabit, abin da ya sa daruruwan mazauna suka tsere daga gidajen su saboda gudun ramuwar gayya.
Fiye da mutane 30 aka kashe a cikin shekara daya a wannan yankin sakamakon tashe tashen hankula na kabilanci da ake fuskanta tsakanin kabilun Borana, Gabra da Rendile. (Fatimah)