Babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya ba da sanarwar cewa, ya nada Philippe Lazzarini a matsayin mataimakin manzon musamman, kuma jami'in dake kula da harkokin jin kai dake Somaliya.
Jami'in, 'dan asalin kasar Swiss, zai kasance mataimakin manzon musamman na sakatare janar MDD, Nicholas Kay dake jagorantar tawagar ayyukan ba da jin kai ta MDD a kasar Somaliya (MANUSOM).
Kafin wannan nadin, mista Lazzarini ya rike mukamai da dama masu muhimmanci a cibiyar daidaita harkokin jin kai (OCHA).
Kwamitin tsaro na MDD ya kafa tawagar MANUSOM a cikin watan Mayun da ya gabata bisa wa'adin farko na watanni goma sha biyu, tawagar ta fara aiki a ranar 3 ga watan Junin shekarar 2013, inda aka aza mata nauyin tallafawa shirin zaman lafiya da sasanta 'yan kasar Somaliya da gwamnatin tarayyar Somaliya take jagoranta ta hanyar taimaka mata da dabaru da shawarwari a wannan fanni, ta yadda za'a samu azamar karfafa zaman lafiya da gina kasar Somaliya. (Maman Ada)