Hukumar lura da 'yan gudun hijira ta MDD, ta ce, za ta tallafawa dinbin 'yan gudun hijirar kasar Somaliya, masu burin komawa gida bisa radin kansu dake sansanin 'yan gudun hijirar kasar Kenya.
A cewar hukumar, za a fara wani kwarya-kwaryar shirin ba da tallafi, ga 'yan gudun hijirar masu muradin komawa yankunansu na asali, tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin sabuwar shekara.
Wata sanarwa daga ofishin lura da tsare-tsaren hukumar ko OCHA a takaice, ta bayyana cewa, kimanin 'yan gudun hijirar Somaliyan 10,000 ne za su amfana daga shirin na watanni 6. Kuma tuni aka fara rijistar masu sha'awar komawa kasar tasu a sansanin Dadaab dake kasar ta Kenya.
Yawan 'yan gudun hijirar kasar ta Kenya dake Dadaab sun kai kimanin mutane 500,000. An kuma kafa wannan sansani ne a shekarar 1991, lokacin da yakin basasa ya barke a kasar ta Somaliya. An ce, adadin 'yan gudun hijirar ya rika karuwa sannu a hankali sakamakon fari, da kanfar abinci da suka rika addabi kasar a lokuta daban daban. (Saminu)