Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi tare da takwaransa na kasar Rasha, Serguei Lavrov sun tattauna ta wayar tarho a ranar Litinin kan fashewar bam da ta faru a Volgograd da batun ziyarar faraministan kasar Japan Shinzo Abe a wurin ibada na Yasukuni.
Mista Wang ya yi allawadai da babbar murya kan harin ta'addanci a birnin Volgograd na kasar Rasha, tare da bayyana cewa, kasar Sin na goyon bayan matakan da kasar Rasha ta dauka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar.
Lavrov, takwaransa na Rasha ya nuna godiyarsa ga kasar Sin, tare da jaddada cewa, kasar Rasha a shirye take wajen kara karfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin, musamman ma wajen yaki da ta'addanci.
A game da batun ziyarar faraministan Japan Shinzo Abe a wurin ibada na Yasukuni mai dauke da masu hannu da jini na yakin duniya na biyu, mista Wang ya bayyana cewa, wannan ziyara ya kamata ta ja hankalin manyan shuagabannin kasashen duniya dake fatan tabbatar da zaman lafiya a duk fadin duniya.
A matsayin kasashen da suka ci nasarar yakin duniya kan Fascist da kuma matsayinsu na zaunannun mambobin kwamitin sulhu na MDD, kasashen Sin da Rasha ya kamata su cigaba da sanya kokari domin aiwatar da dokar kasa da kasa da tsarin duniya bayan yakin duniya na biyu, in ji mista Wang. (Maman Ada)