in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Isra'ila ya bayyana tabbacin cimma yarjejeniyar samar da zaman lafiya da Falesdinu
2013-12-09 11:03:59 cri
A ranar 8 ga wata, shugaban kasar Isra'ila Shimon Peres ya bayyana cewa, yana da tabbacin cimma yarjejeyiyar zaman lafiya tsakanin kasarsa da Falesdinu cikin watanni masu zuwa.

A gun bikin bude taron kasuwanci na shekara-shekara na kasar Isra'ila, shugaba Peres ya bayyana cewa, a cikin watanni masu zuwa, ya yiwu za a cimma yarjejeniyar samar da zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila, amma, akwai sharadi, wato dole ne Falesdinu ta amince da Isra'ila a matsayin kasar Yahudawa kuma ta tabbatar da tsaron kasar.

Ya kuma bayyana cewa, Isra'ila ta taba janyewa daga zirin Gaza, amma hakan bai samar da zaman lafiya ba, kuma har yanzu jama'arta suna fuskantar harin rokoki daga yankin Gaza. Gwamnatin Isra'ila ba za ta amince da sake aukuwar irin wannan lamarin da ke kawo barazana ga tsaron kasa da ke faruwa a yankin da ke yammacin gabar kogin Jordan ba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China