Wannan taro dai an gudanar da shi ne a babban filin wasa dake birnin Damaturu wanda ya samu halartar dukannin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC a jihar Yobe, ciki har da gwamna Alhaji Ibrahim Geidam da sauran jiga-jigan gwamnatin jihar da magoya bayan jam'iyyar daga dukkan sassan jihar, hade da sababbin membobin jam'iyyar fiye da dubu 10 da suka canza sheka daga jam'iyyar PDP suka dawo sabuwar jam'iyyar ta APC daga shiyyoyi uku na jihar.
Lokacin da yake bayani a wajen taron gangamin, gwamnan jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam ya bayyana cewa, wannan gangami da suka gudanar na bayar da tuta ga 'yan takarar mukamin shugabannin kananan hukumomin jihar, ikon Allah ne, hakan ya nuna cewa lalle akwai zaman lafiya a jihar da har hakan ya ba su damar gudanar da zabe, sabanin maganganun da wasu makiya jihar ke cewa, wai babu zaman lafiyar da zai sa a iya gudanar da zabe a jihar.
Gwamna Geidam ya kuma yi kira ga dukkannin 'ya'yan jam'iyyar ta APC da su zama tsintsiya madaurinki daya su yi tsayin daka wajen ganin sun fito kwansu da kwarkwata don kada kuri'unsu a zaben da za'a gudanar gobe Asabar. Alhaji Geidam ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da kar su sa kansu a harkokin siyasa, inda ya ce harkokin siyasa na 'yan siyasa ne, harkokin tsaro kuma na jami'an tsaro ne, don haka su tsaya akan aikinsu kawai, kana ya yaba musu kan yadda suke gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro a jihar.
Jiga-jigan jam'iyyar ta APC da masu rike da madafun iko dake jihar da yawa sun yi jawabai wadanda duka suka nuna cewar sun goyi bayan abubuwan da jagoransu gwamna Gaidam yake yi don ciyar da jam'iyyar APC da jihar gaba.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.