Sanarwar ta ce, a daren ranar 20 ga wata, shugaba Obama ya saurari takaitaccen bayani dangane da jikkatar sojojin Amurka hudu a yayin da suke gudanar da aikin kwashe mutanen Amurka daga Sudan ta Kudu. Haka kuma a wannan rana, mista Obama ya tattauna da manyan jami'an tsaron kasar Amurka ta hanyar tarho, inda ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin Amurka da MDD kan ba da kariya ga mutanen Amurka a ketare, tare da bukatar kasar Sudan ta Kudu da ta dauki alhakin tabbatar da tsaron mutanen Amurka dake kasar. Ya ce, ba za a iya daidaita rikicin Sudan ta Kudu ba, sai ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. Kamata ya yi bangarorin daban daban su kara kokarin sa kaimi wajen gudanar da shawarwarin zaman lafiya tsakaninsu domin magance abkuwar riciki.
A ranar 21 ga wata kuma, hukumar bada umurni ta sojan Amurka a Afirka ta tabbatar da cewa, an kai hari kan wani jirgin saman sojan Amurka a wannan rana yayin da yake kan hanyarsa ta zuwan kwashe mutanen Amurka daga birnin Bor na jihar Jonglei dake arewacin kasar Sudan ta Kudu, hakan ya haddasa jikkatar sojojin hudu, lamarin da ya kai ga dakatar da wannan aiki daga karshe. (fatima)