Yang ya yi wannan bayani ne sa'ilin da ya gana da Hillary Clinton, takwararsa ta Amurka, a gefen muhawarar dake gudana a babban zauren MDD.
Ya ce, gurguwar shawarar Amurka ta sayar da makamai ga Taiwan, ta sabawa kuduri uku na takardun hadin gwiwa tsakanin Amurka da Sin da takardar bayan taron ranar 17 ga watan Agusta, tare da yin kutse ga harkar cikin gidan Sin, sannan karan tsaye ne sosai ga harkar tsaron Sin da ma kokarin da take yi na samun hadin kan kasa har da dangantakarta da Amurkar.
Hillary Clinton, sakatariyar harkokin wajen Amurka ta ce, kasarta tana kokarin fadada, zurfafa da samar da sahihiya kana cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa da Sin
Ta kuma kara da cewa, Amurka tana kiyaye manufar kasar Sin daya tak a doron kasa, kana tana lura da matsayin Sin da damuwarta game da cinikin makamai tsakanin Amurka da Taiwan. (Garba)