Gwamantin jihar Kano a arewacin Najeriya ta tsara zata kashe sama da naira buliyan 219 a kasafin kudinta na 2014
|
A ranar talata daga gabata ne Gwamnan Kano Rabi`u Musa Kwankwaso ya gabatar da kasafin kudin sa gaban majalissar dokokin jihar, inda ya yi alkawarin karasa ayyukan daya faro shekara ta 2013.
Kasafin kudin jihar Kanon na bana ya nuna baza`a gudanar da wani sabon aiki ba a cikin sabuwar shekara mai kamawa.
Dr. Rabi`u Musa kwankwaso wanda a karon farko ya gabatar da kasafin kudin cikin dare, ya shafe sama da sa`oi biyu ya karanta jawabin kasafin kudin mai shafuka 35, ya bugi kirjin cewa babu wata jiha da tsarin kasafin kudin ta ya kama kafar na jihar Kano ta fuskar inganci.
Gwamnan wanda ya fara da zayyano irin nasarorin daya samu cimmawa a kasafin kudin 2013, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta samu cimma nasarar kaso 75 na ayyukan data bijiro dasu, wanda ba kasafai ake samun haka ba a tarayyar Najeriya.
Inijiniyar Rabi `u Musa Kwankwaso ya ce sun cimma wadannan nasarori ne sakamakon kaucewa ciwo bashi daga waje dama cikin gida, a maimakon hakan gwamnati ta ga dacewar ririta dan abun dake hannun ta wajen yiwa jama` a aiki.
Kamar yadda kasafin kudin na badi ya nuna ma`aikatar ayyuka da sufuri itace mai kaso mafi tsoka, inda ta tashi da tsabar kudi sama da naira buliyan 81, sai bangaren ilimi wanda yake da naira buliyan 20.85
A wannan gabar ce Gwamna Kwankwaso ya sanar da cewa tuni gwmanatin sa ta kammala shirye shiryen fara bayar da ilimi kyauta ga `yan asalin jihar a matakan firamare da sakandire da kuma manyan makarantun gaba da sakandire mallakar gwamnatin jihar, kari akan daukar nauyin dalubai `yan jihar zuwa kasashen wajen domin kara fadada ilimi kyauta.
Yace wannan shiri zai fara aiki daga sabuwar shekarar nan mai zuwa.
Haka zalika gwamnan na jihar Kano ya kara dacewa daga cikin nasarorin da gwmanatin sa ta samu shi ne rage bashin da ya gada kasashen waje na bin gwamnati na sama da naira buliyan 70, wanda yanzu ya dawo naira buliyan 32.(Garba Abdullahi Bagwai)