Kwamishinan kudin jihar Ebonyi dake Kudu maso Gabashin Najeriyar Timothy Odah ne ya tabbatar da hakan, yayin da yake zantawa da 'yan jaridu, game da sakamakon taron wata wata da kwamitin rabon tattalin arziki kasa, wanda kwamishinonin kudin jihohin kasar ke gudanarwa.
Odah ya ce daya daga kusoshin kamfanin ne ya tabbatar wa kwmishinonin wannan zargi yayin taron su na wannan wata, kuma jami'in na NNPC ya ce za a bayyana hakikanin yawan kudaden da ake batu kan su yayin taron kwamitin na wata mai zuwa.
Tun da fari dai babban bankin kasar CBN ne ya furta cewa, kamfanin NNPCn bai sanya wasu kudi da yawan su ya haura dalar Amurka miliyan dubu 49 cikin lalitar gwamnatin kasar ba, zargin da a baya kamfanin ya karyata.(Saminu Alhassan)