Gwamantin jihar Kano a arewacin Najeriya ta tsara zata kashe sama da naira buliyan 219 a kasafin kudinta na 2014
|
Gwamnatin jihar Gombe dake arewacin tarayyar Najeriya, ta sanar da ware kudi har Naira biliyan 1.9, domin bunkasa harkokin da suka shafi mata da matasa a shekara mai kamawa
Kunshin kasafin kudin dai wani bangare ne na kasafin kudin jihar ta Gombe na shekara ta 2014, da zai lashe kudi har Naira miliyan dubu dari daya da bakwai da digo 4, wanda gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Dankwambo ya mikawa majalissar dokokin jihar a jiya Jumm'a 27 ga wata.
Gwamna Dankwambo ya ce, Naira biliyan 1.1 za'a yi amfani da ita ne, wajen horar da mata sana'oi karkashin ofishin shirin bunkasa rayuwar matan jihar na HAWEP, Shirin da a cewar gwamnan jihar zai taimakawa mata wajen taka rawar a-zo-a-gani, ta fuskar habaka tattalin arzikin jihar. Haka kuma ya ce jiharsa zata yi iyakacin kokari wajen kawar da duk wani bambancin da ake nunawa mata.
Har wa yau kuma, Alhaji Dankwambo ya ce, gwamnatinsa zata tsara wani muhimmin shiri na tallafawa tsofaffi gami da nakasassu, wanda ake kira PWDS.
A fannin raya harkokin matasa kuma, gwamnan ya ce, za'a yi amfani da Naira miliyan dari bakwai da casa'in da shida, domin raya harkokin matasa da yaki da fatara, da kuma horas da matasan fannoni sana'oi daban-daban, a wani kokari na samar musu da guraban ayyukan yi.
Har wa yau Alhaji Dankwambo ya ce, za a kashe Naira miliyan 820, a fannin raya harkokin motsa jiki a dai shekara ta 2014..(Murtala)