1104murtala.m4a
|
Da safiyar yau Litinin 4 ga wata ne, wata gobara ta tashi a wani ginin dake kasuwar Marina dake tsakiyar birnin Ikko. Wakilinmu Murala dake Lagos yana dauke da karin bayani.
Kasuwar Marina, wata babbar kasuwa ce da ake sayar da tufafi, kayan hannu, kayan gida, kayan lantarki da saurasu a tsibirin Legas na birnin Ikko, wato Lagos Island. Gobarar ta tashi ne a wani gini mai suna Great Nigerian Building dake kasuwar ta Marina.
Lokacin da na isa gurin, na ga ma'aikatan kashe gobara da yawa suna kokarin fesa ruwa ga ginin da ya kama da wuta. Na kuma zanta da mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA dake birnin Ikko, Ibrahim Farinloye, inda ya ce: "Da misalin karfe 6 da minti 32 ne muka samu labarin cewa, gobara ta tashi a wannan wuri, kuma ba tare da wani jinkiri ba muka tura 'yan kwana-kwana don su kashe gobarar. Haka kuma mun tuntubi babban hafsan tsaron Najeriya don ya turo sojoji domin su karbi aikin. Na yi imanin cewa za mu shawo kan gobara in sha Allahu."
Bayanai na nuna cewa, akwai shaguna da yawa a cikin wannan gini wato Great Nigerian Building dake kasuwar Marina, ciki har da wasu shagunan 'yan kasuwan kasar Sin masu zaman kansu.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba mu samu karin bayani dangane da hasarar dukiya ko rayuka sanadiyar wannan gabara ba. (Murtala)