in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar dokokin jihar Taraba da ke Najeriya ya mutu
2013-11-04 19:56:02 cri
A yau Litinin ne shugaban majalisar dokokin jihar Taraba da ke tarayyar Najeriya Haruna Tsokwa ya riga mu gidan gaskiya.

Mista Tsokwa ya mutu ne a safiyar ranar yau Litinin a cibiyar lafiya ta tarayya, wato Federal Medical Centre dake Jalingo, babban birnin jihar Taraba, bayan ya yi fama da wata gajeriyar rashin lafiya

Mamacin ya kwanta rashin lafiyar ne a ranar Alhamis da ta gabata.

Kefas Sule, mai magana da yawun mukaddashin gwamnan jihar Taraba Garba Umar ya tabbatar da mutuwar Haruna Tsokwa, inda ya ce gwamnatin jihar Taraba ba za ta yi karin bayani ba sai likitan mamacin ya fitar da rahoto game da ainihin musabbabin rasuwar tasa.

Marigayi Haruna Tsokwa na daya daga cikin wadanda magoya-bayan ganin Garba Umar ya ci gaba da jagorantar jihar Taraba tun bayan da gwamna Danbaba Suntai ya dawo daga jinya, amma ba tare da ya samu sauki gaba daya ba.

Ko a baya wato ranar 19 ga watan Satumban bana, 'yan bindiga sun taba kaiwa ayarin motocin Tsokwa farmaki inda ya tsallake rijiya da baya, bayan da aka yi musanyar wuta tsakanin 'yan bindigar da masu tsaron lafiyarsa.

Marigayi Haruna Tsokwa yana da mata daya da 'ya'ya hudu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China