Mista Ban ya ce yana matukar allawadai da abun bacin rai na harin da aka kaiwa sansanin MDD dake Aboko a ranar 19 ga watan Disamba, da ya hallaka sojojin MDD biyu a yayin da suke kokarin kare fararen hula da suka nemi mafaka wajensu.
A kalla fararen hula 20 ne da suka samu mafaka a sansanin MDD aka kashe a ranar Alhamis a wani harin da aka kai a Aboko dake jihar Jonglei.
MDD ta tabbatar da mutuwar sojojin MDD biyu 'yan kasar Indiya a ranar Jumma'a, bayan ta samu wannan labari daga tawagarta dake kasar Sudan ta Kudu.
Haka zalika, Ban Ki-moon ya bukaci shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da shugabannin adawa na kasar, musamman ma tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar dasu koma teburin shawarwari domin cimma wata mafitar siyasa da zata kawo karshen wannan rikici.
Ita ma a nata bangare, kungiyar tarayyar Afrika AU, ta yi kira ga bangarori dake gaba da juna a kasar Sudan ta Kudu dasu dakatar da bude wuta nan take.
Shugabar kwamitin tarayyar Afrika, Nkosazana Dlamini Zuma, tana nuna fargabarta sosai kan halin da ake ciki a wannan kasa a cewar wata sanarwa ta kungiyar, dake yin kashedi game da barkewar wani yakin basasa a cikin wannan sabuwar kasa da aka kafa yau da shekaru biyu da rabi da suka gabata.
Madam Dlamini-Zuma ta yi kira ga kwamitin tsaro da zaman lafiya na tarayyar Afrika da kuma jam'iyyun siyasa na kasar Sudan ta Kudu dasu taimakawa wajen hana wannan kasa fadawa cikin rikicin yakin basasa. Haka kuma jami'ar ta nuna babbar damuwarta kan tabarbarewar matsalar jin kai a kasar Sudan ta Kudu. (Maman Ada)