Ranar 25 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Turkiya Ahmet Davutoglu ya yi hira da manema labaru kan batun bukatar da kasarsa ta gabatarwa kungiyar NATO dangane da girka makamai masu linzami a bakin iyakar dake tsakanin Turkiya da kasar Sham, inda ya ce, babu bukatar kasar Rasha da Iran su nuna damuwa kan cewa, lamarin zai kara tsanantar da halin da ake ciki a kasar Sham.
Mista Davutoglu ya ce, za a girka makamai masu linzami ne da zummar tsaron kasar Turkiya. Turkiya ba ta fuskanci duk wata barazana a fannin tsaro ba, to ba za ta yi amfani da wadannan makamai ba. Amma an dorawa gwamnatin kasar Turkiya nauyin daukar dukkan matakai da suka dace domin mayar da martani ga hare-haren da za a kai mata.
Ban da haka, ya ce, idan an sassauta rikicin da Turkiya take fuskanta a kan iyaka, to, za ta kawar da wadannan makamai.
Kwanan baya, ana fuskantar rikici mai tsanani kan iyakar dake tsakanin Turkiya da Sham. Kuma Turkiya ta kai harin roka da dama kan wasu wuraren kasar Sham domin mayar da martani kan harin da aka kai mata daga Sham. (Amina)