Bisa labaran da aka samu daga kafofin watsa labaran kasar, an ce, a ran 22 ga wata da safe, an harba bindigogi masu luguden wuta ga yankin Mazzeh da ke birnin Damascus, a sanadin haka, mutane da dama sun jikkata, kuma a dai wannan rana, wani bam dake cikin wata mota ya fashe a yankin Badze na birnin.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaran kasar ta Syria ya samar, an ce, a cikin wannan rana kuma, wani 'dan jarida dake aiki a gidan talabijin na kasar ta Syria ya rasu bayan da wasu dakaru sun yi garkuwa da shi a Tadamun, dake karkarar Damascus. Daga bisani dai, kungiyar 'yan adawar kasar ta bayar da wata sanarwa inda ta nuna cewa, za ta dauki alhakin mutuwar wannan 'dan jarida.
Wani jami'in kungiyar adawa ta Syria ya nuna cewa, a cikin wannan rana, sojojin gwamnatin kasar ta Syria sun ci gaba da yin musayar wuta mai tsanani da dakarun kungiyar adawa wato sojojin 'yantar da kasar ta Syria a karkarar da ke kudancin Damascus, bugu da kari, mutane da dama sun jikkata a sanadiyar farmaki na bindigogi da ya faru a yankin da ke kusa da babbar hanya tsakanin Damascus da Daraa na kudancin kasar.
Ban da wannan kuma, a ran 22 ga wata, kan batun sanya wa iyakar kasa tsakanin Syria da Turkiya kariyar makamai masu linzami na "Patriot" bisa wani kiran da Turkiya ta yi wa kungiyar NATO, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Alexander Lukashevich, ya ce, ya kamata Turkiya ta matsa lamba ga kasar Syria, ta yadda za a iya tabbatar da shawarwari tsakanin bangarorin da ke gwabzawa da juna na kasar, amma, Turkiya ta zabi wata hanya daban wadda za ta iya zama hadari gare ta.(Maryam)