Wasikar ta bayyana kiyaye tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan asalin kasar ta Amurka, a matsayin babban dalilin aikewa da dakarun. An kuma ce wadannan sojoji za su koma Amurka da zarar al'amura sun daidai ta a kasar.
Cikin 'yan makwannin nan dai, tashe-tsahen hankula a kasar Sudan ta Kudu sun haddasa mutuwar mutane kimanin dubu guda. Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya zargi tsohon ma'aimakin sa Riek Machar da shirya juyin mulki, wanda daga baya ya janyo dauki ba dadi tsakanin sassan kasar da basa ga maciji da juna, koda yake dai Machar ya karyata wannan zargi. (Maryam)